Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Najeriya na yin asarar tan miliyan 1.8 na Tumatir duk shekara – Ministan Noma - Martaba FM Najeriya na yin asarar tan miliyan 1.8 na Tumatir duk shekara – Ministan Noma - Martaba FM

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana cewa Najeriya na asarar fiye da kashi 45 cikin 100 na amfanin tumatir da ake nomawa a ƙasar duk shekara.

Wannan dai na faruwa ne saboda matsalolin ɓarnatar da amfanin gona bayan girbi da kuma gazawar tsarin rarraba kayan gona.

Kyari, wanda Daraktan Ma’aikatar Noma, Ibrahim Alkali, ya wakilta a wajen ƙaddamar da cibiyar GB Hub Africa a Abuja, ya ce Najeriya na samar da tan miliyan 3.997 na tumatir a kowace shekara, amma tan miliyan 1.8 daga ciki na lalacewa.

“Wannan asarar ta na nufin ba wai abinci kawai ne ke lalacewa ba, har da hanyoyin samun aiki, arziƙi da kuma abinci mai gina jiki ga ƴan ƙasa,” in ji shi.

Ya bayyana cewa duk da Najeriya na matsayin ƙasa mafi yawan noman tumatir a Afirka, ita ce kuma mafi yawan shigo da gyaran tumatir daga ƙasashen waje a duniya. Ya ce matsalolin da ke haddasa hakan sun haɗa da rashin isassun kayan sarrafa amfanin gona, rashin haɗin kai tsakanin manoma da masana’antun sarrafa kaya, da kuma amfani da tsofaffin hanyoyin noma.

“Gazawar haɗa manoma da kamfanonin da za su sarrafa kayan amfanin su ya ƙara dagula lamarin,” in ji Kyari.

A cewarsa, hakan na hana bunkasar tattalin arzikin noma da kuma rage yawan kayan amfanin gida da ake iya sarrafawa.

Rahoton ya bayyana cewa manoman tumatir na fuskantar barazana daga wata ƙwari mai suna *Tuta Absoluta* – wadda ake kira Tomato Leaf Miner – wacce ke yaduwa cikin sauri kuma na iya hallaka dukan amfanin gona idan ba a yi mata magani da gaggawa ba.

Ministan ya yaba da kamfanin GBFoods bisa kafa babbar masana’antar sarrafa tumatir a jihar Kebbi, wacce ke da ƙarfin sarrafa tan 25,000 na tumatir a kowace shekara.

Ya ce, irin waɗannan masana’antu ne ƙasar ke bukata domin rage dogaro da kayayyakin abinci daga waje da kuma inganta rayuwar manoma a ƙasar.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *