Daga Sani Ibrahim Maitaya
Rundunar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Zamfara ta tura jami’ai dari hudu da goma sha biyar (415) a fadin jihar, a wani mataki na tabbatar da tsaro yayin bukukuwan Easter na shekarar 2025.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASCII Umar Mohammad M. ya fitar a ranar Alhamis, tura jami’an ya shafi wuraren ibada da wurare masu muhimmanci a kananan hukumomi goma sha hudu (14) na jihar.
Wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen hukumar na samar da tsaro a lokacin bukukuwan, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga mazauna jihar yayin wannan lokaci.
Sanarwar ta ruwaito Kwamandan Sani Mustapha yana cewa, wannan tura jami’an yana da nasaba da hangen nesa na Babban Kwamandan NSCDC na kasa Dr. Ahmed Abubakar Audi, OFR, mni, wanda ke ci gaba da jaddada mahimmancin kwarewa, sadaukarwa da inganci wajen magance matsalolin tsaro a kasar nan.
“A bisa umarnin Babban Kwamandan, rundunar NSCDC ta jihar Zamfara ta shirya tsaf domin kare rayukka da dukiyoyi a wannan lokacin na bukukuwan Easter. Mun tura jami’an mu zuwa wuraren da suka dace domin tabbatar da doka da oda tare da fuskantar duk wani lamari na gaggawa da ka iya tasowa,” in ji Mustapha.
Ya kara da tabbatar wa you mazauna jihar cewa, rundunar za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro don ganin an gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali.
NSCDC ta kuma bukaci jama’a da su hada kai da jami’an tsaro tare da kai rahoton duk wani al’amari da ake zargi zuwa ofishin tsaro mafi kusa.
Sanarwar ta kammala da jaddada kudirin rundunar na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar Zamfara.