Tsohon Sanata kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam Sanata Shehu Sani, ya yi gargadi mai karfi ga Shugaba Bola Tinubu, yana mai bukatar ya guji fadawa cikin tarkon son kabilanci a harkar mulki.
Da yake magana kan suka da dama da ake yi wa gwamnatin Tinubu, Sani ya bayyana hakan ne a wani shirin kai tsaye na Channels TV mai suna “Politics Today” a ranar Alhamis.
Ya tambayi dalilin yin shiru na mutane da dama a lokacin da ya ce akwai tsananin rashin tsaro da son kai a mulkin Buhari.
Ya ja kunnen Tinubu da kada ya bi irin wannan tafarki na son kai da ya bata wasu gwamnatoci a baya.
“Wannan yana nufin cewa Shugaba Asiwaju ya zama mai taka tsantsan. Kada ya bi wannan hanya domin hakan ya zama ruwan dare a siyasar Afirka. Don haka wadanda suka samu mulki su dauke shi a matsayin damar yi wa kasa hidima, ba kamar wadanda suka ci nasara a yaki ba kuma sai su mayar da hankali wajen faranta ran kabilar su kadai.”
“Idan za a yi magana a kan wannan gwamnati, mutum ya tambayi kansa, Daga ina muke zuwa? Me ya sa mutum ya yi shiru? A lokacin da ake kashe-kashe a mulkin Buhari, wato rashin tsaro, lokacin ne aka fi samun tsanani fiye da kowanne lokaci,” in ji Sani.
Ya kara da cewa duk da matsalolin da ake fuskanta yanzu, musamman rashin tsaro a wasu yankuna kamar Filato da Binuwai, akwai gagarumin ci gaba idan aka kwatanta da gwamnatin da ta gabata.
“Ba wai ina magana da yawun gwamnati ba. Amma yaushe aka ji wani hari a makarantu a arewacin Najeriya da aka sace dalibai? Me muke da shi yanzu? Daga Kaduna zuwa Abuja, yaushe aka ji an kai hari ko sace mutane? Hakan baya faruwa yanzu. Amma ba yana nufin kasar ta samu cikakken tsaro ba, musamman da abinda ke faruwa a Filato da Benue,” in ji shi. “Amma idan aka kwatanta da baya, mun yi gaba. Ko da ba mu kai inda muke bukata ba.”
Game da zargin son kai wajen nada mukamai a gwamnatin Tinubu, Sani ya bayyana yadda hakan ya kasance a fili a zamanin Buhari.
“A bangaren tattalin arziki me ya faru? Me ya faru a mulkin Buhari dangane da son kai? Mutane fiye da nade-nade 30 aka baiwa mutanen Katsina a wancan lokacin, da kuma mambobin hukumomi 50.” Inji shi.
Ya yi gargadi kan yin amfani da kabilanci idan aka samu sauyin gwamanti.