Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya ta bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da gudanar da ayyukansa na shugabanci duk da kasancewarsa a ƙasashen Turai na ɗan lokaci.
A wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, an tabbatar da cewa tafiyar shugaban ƙasa na cikin jadawalin da aka sanar tun farko na kusan makonni biyu kacal.
Sanarwar ta bayyana cewa shugaban ƙasa ya bar birnin Paris zuwa London a ƙarshen mako, in da ya ke ci gaba da tuntubar manyan jami’an gwamnati akai-akai. Har ila yau, ya na bai wa shugabannin tsaro umarni game da yadda za su tinkari sabbin barazanar tsaro da ke fitowa a wasu sassan ƙasar.
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa ana sa ran Shugaba Tinubu zai koma Abuja tare da ci gaba da aiki a fadar Aso Villa bayan kammala hutun bikin Easter.
Sanarwar ta ƙara da cewa shugaba Tinubu ya na da cikakken kwarin guiwa da jajircewa wajen aiwatar da nauyin da ke kansa, kuma gwamnatin na ci gaba da aiki yadda ya kamata a ƙarƙashin jagorancinsa.
Daga ƙarshe, fadar shugaban ƙasa ta nuna godiya ga damuwar jama’a tare da tabbatar wa ’yan Najeriya cewa babu tangarda a harkokin mulki duk da tafiyar shugaban na ɗan lokaci.