Tsohon ɗan wasan gaba na Ingila John Fashanu, ya kai ƙarar Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya yana neman diyya ta yiro £100,000 bayan da aka kama shi bisa wasu zarge-zarge daban-daban.
Ana zargin Fashanu da laifuka kamar haɗa baki don aikata laifi, barazana ga rayuwa, tsoratarwa, da kuma kutse.
Sai dai ɗan wasan mai shekaru 62 ya musanta waɗannan zarge-zarge kwata-kwata, yana mai cewa matsalar ta samo asali ne daga gardamar filaye da ke tsakanin sa da wasu masu zuba jari da suka amince su biya fiye da £500,000, domin mallakar filin sa mai girman eka 22.
A cewar jaridar The Mirror, an kama Fashanu ne bayan da ya tambayi wasu yan kwangila da ke gina shinge a filin sa.
Fashanu ya yi ikirarin cewa shi da matar sa Vivian da lauyan su sun fuskanci “kamawa, da tsarewa, da kuma cin zarafi na tsawon kimanin sa’o’i ukku a ranar 16 ga watan Disamba.
Ya kuma zargi ‘yan sanda da take masa hakki, ta hanyar “takura masa a kai a kai” da kuma “sabon wariyar doka da ya ci karo da kundin tsarin mulkin ƙasa.”
Lauyan sa Mista Chigbu, ya tabbatar da cewa: “Dukkan su ukku sun cika sharuddan beli kuma ‘yan sanda sun sake su bisa belin.”
John Fashanu wanda ya buga wa ƙungiyoyin Norwich City, Wimbledon, da Aston Villa, ya kasance gwarzo a ƙungiyar Wimbledon lokacin da suka lashe kofin FA a 1988,kuma ya wakilci Ingila a wasanni biyu na ƙasa da ƙasa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya