Jagoran ‘yan uwa Musulmi a Kaduna da aka fi sani da ‘yan Shi’a karkashin Jagorancin sheikh Ibrahim Elzakzaky, Malam Aliyu Umar Tirmidhi ya shaida wa BBC cewa ‘yan sanda sun far musu tare da buɗe musu wuta ba tare da wani dalili ba, inda suka kashe mutum biyar da jikkata 25, a lokacin da suke gudanar da tattakin nuna goyon baya ga Falasɗinawa jiya Juma’a, a birnin Kaduna.
“Muna cikin tattakin lami lafiya kawai sai muka ji ana harbe-harbe a bayanmu, hakan ya sa muka yi addu’a muka ce kowa ya tafi gida, ai kuwa kawai ƴan sanda suka kara buɗe wuta inda suka shahadantar da mutum biyar da jikkata 25.”
Mabiya sheikh Zakzaky dai kan gudanar da tattakin nuna goyon baya ga Al’ummar Falasɗinawa a duk juma’ar karshen watan Ramadan.
Malam Tirmidhi ya kuma ce a Zaria ma ‘yan sandan sun harbe mutum ɗaya ya kuma ya yi shahada.
Dangane kuma da waɗanda aka kama, malam Tirmidhi ya ce yanzu haka suna haɗa alkaluma domin tantance yawansu amma dai sun hakkake cewa a yanzu mutum shida suna hannun ‘yan sanda.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna dai ta bakin mai magana da yawunta, ASP Mansir Hassan, ta ce “mutanen sun fito ɗauke da makamai kuma suka far wa al’ummar gari wannan ya sa muka tarwatsa su sannan mun kama wasu za mu gurfanar da su a kotu.”
To sai dai malam Tirmidhi ya ce wannan maganar ba gaskiya ba ne.
“Mu da muka fito mata da maza sannan kanana da manyanmu wato kwanmu da kwarkwata yaya za a yi mu ɗauki makami har mu fara far wa jama’a? Ai hankali ba zai ɗauka ba.”
BBC Hausa