October 16, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Za Mu Yi Ƙoƙarin Rage Kuɗin Aikin Hajjin Bana – NAHCON.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Yayin da maniyata aikin hajjin bana a Najeriya ke cikin rashin tabbas kan tsadar kujerar zuwa ƙasa mai tsarki don sauke farali, shugaban hukumar jin daɗin alhazai NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya ce hukumar tana ƙoƙari domin tabbatar da kuɗin Hajjin bai kai yadda ake hasashe ba, in da ya ce abin da yake fata shi ne raguwa.

Gwamnatin Tarayya ba za ta saka tallafi a kuɗin aikin Hajjin 2025 ba,-NAHCON.

Hukumar Kula Da Shige Da Fice Ta Najeriya Ta Yi Ƙarin Girma Ga Wasu Jami’anta A Jihar Gombe.

Fadar Shugaban Najeriya Ta Karrama Shugaban Makarantar Sakandare A Jihar Zamfara.

BBC ta rawaito, hukumar ta sanar da cire tallafin da ta ke bayarwa a kan kuɗin Hajjin duk shekara, wanda a sanadiyar hakan masana suka ce kuɗin kujerar Hajjin zai iya haura naira miliyan 10.

Sabon shugaban hukumar, Saleh Usman, wanda aka fi sani da Saleh Pakistan ya ce, “ba ma fatan a samu ƙarin kuɗin kujerar Hajji kamar yadda ake hasashe, za mu yi duk mai yiwuwa wajen ganin hakan bai faru ba, kuma muna fata in sha Allah ba zai kai haka ba.

“Abin da muke fata shi ne a samu ragowa daga farashin kuɗin kujerar da aka biya a bara, kuma muna fata da yardar Allah za mu samu nasara.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *