Labarai

Ƴan bindiga sun kai hari gidan yari a Cross River, tare hallaka Jami’in tsaro ɗaya

Ƴan bindigar sun bude wuta ne a kan jami’an tsaro na hadin gwiwa da ke gidan yarin

 

A jiya Laraba da daddare ne aka kashe wani jami’in gidan gyaran hali a lokacin da wasu ƴan bindiga su ka kai hari a gidan gyaran hali na Afokang da ke Calabar a jihar Cross River.

Kakakin rundunar ƴansanda a jihar, Affanga Etim, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Calabar a yau Alhamis.

Sai dai ya musanta ikirarin cewa an kai harin ne a ginin gidan gyaran halin.

Ya kara da cewa ƴan bindigar sun bude wuta ne a kan jami’an tsaro na hadin gwiwa da ke wurin, kuma babu wata barna da aka samu a wurin.

A cewarsa, “Lokacin da suka zo, sai suka bude wa jami’an tsaron wuta da su ma suka mayar da martani, kuma a cikin haka ne aka kashe wani mataimakin Sufeto, ASC.

Babu fursuna ko daya da ya tsere ko aka kashe, maharan ba su kusanci ma wurin ba.

“A yayin da muke magana, mun tura karin jami’ai dauke da makamai zuwa wurin kuma komai ya dawo daidai.”

Daily Nigerian Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button