Labarai
Trending

Ƴansanda Sun Cafke Wani Direba Ɗauke Da Bindigu Da Wasu Makamai A Jihar Legas.

Daga Yusuf Aliyu Umar Gwammaja

Ƴansandan Najeriya a jihar Lagas da ke kudancin ƙasar sun kama wani direban mota ɗauke da bindigu da wasu makamai.

Kakakin rundunar Ƴansanda a jihar SP Benjamin Hundeyi, ne ya tabbatar da kama wanda ake zargin mai suna Azeez Babatunde, a ranar Alhamis ɗinnan.

“Da misalin karfe biyar na safiya ne, jami’an da ke yaƙi da aikata manayan laifuka na Ƴansanda, na ofishin Ƴansanda da ke Makodo,suka gano yadda direban ya yi juyowar gaggawa,zuwa titin Hakeem Dickson,wanda hakan tasa jami’an suka bi bayansa inda suka cafke shi”, in shi.

Ya kuma ce, jami’an rundunar sun kama wani mutum daya,da ya rage a cikin motar tare da direban motar, inda a yayin gudanar da bincike a motar aka gano ƙananan bindigun gami da bindigu kirar gargajiya da kuma wuƙa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button