Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Ƴansandan jihar Kaduna sun ƙaryata tashin wani abun fashewa - Martaba FM Ƴansandan jihar Kaduna sun ƙaryata tashin wani abun fashewa - Martaba FM

Daga Sani Ibrahim Maitaya

Rundunar Ƴansandan jihar Kaduna ta musanta rahotanni na tashin wani abu mai fashewa da aka ce ya faru a yankin Titin Josawa na Abakpa a Kaduna, inda aka ce wani yaro mai shekara 12 ya rasu sannan wasu guda bakwai sun samu raunukka a wani hatsarin bindiga.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar DSP Mansir Hassan ya fitar a ranar Talata, rundunar ta karbi kiran gaggawa game da tashin bama-baman a yankin, amma bayan kammala binciken farko an gano cewa, sabanin rahotannin lamarin ya faru ne sakamakon fitar bindigar dane.

“A ranar 22 ga watan Afrilu 2025 da misalin karfe 0830hrs, ‘Yan Sandan suka karbi kiran gaggawa game da wani hadarin tashin wani abu a yankin Titin Josawa na Abakpa Kaduna.

“A cikin gaggawa, wata tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin DPO na Kawo, an tura su kai tsaye zuwa wurin”.

“Hadarin ya yi sanadiyyar mutuwar wani yaro mai suna Abubakar Muhammed daga Titin Josawa. Haka kuma, wasu mutane bakwai sun samu raunukka daban-daban kuma suna samun kulawar likitoci a halin yanzu.

“Kwamishinan ‘Yan Sanda, Kwamandan Garrison, Daraktan Hukumar Tsaro ta DSS, da kuma shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta arewa sun ziyarci wurin, inda aka gudanar da cikakken bincike a wajen.

“Sabanin rahotanni na farko, kwararru sun tabbatar da cewa wannan ba tashin bam bane. Binciken farko da aka gudanar daga hukumar dake kula da sashen yaki da bama-bamai ya nuna cewa, tashin bindigar dane ne ya jawo mutuwar yaron.

“Ana ci gaba da bincike da kuma tantancewa domin gano cikakken yadda lamarin ya faru”.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *