Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Ƴansandan jihar Kano sun tsare amaryar da ta hallaka angonta kwanaki 9 da aure - Martaba FM Ƴansandan jihar Kano sun tsare amaryar da ta hallaka angonta kwanaki 9 da aure - Martaba FM

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta kama wata mata mai shekaru 18 mai suna Saudat Jibril bisa zargin kashe mijinta, Salisu Idris, ta hanyar yanke masa wuya da wuka mai kaifi.

Lamarin ya faru ne a unguwar Farawa, cikin karamar hukumar Tarauni, da misalin ƙarfe 12:35 na dare, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta bayyana.

A cewar sanarwar: “Wadda ake zargin, Saudat Jibril, nai shekara 18 daga unguwar Farawa , ta yanka wuyan mijinta Salisu Idris, mai shekaru 30, da wuka mai kaifi.”

Kwamishinan Ƴansanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya aika da tawagar Ƴansanda zuwa wurin da lamarin ya faru domin daukar matakin gaggawa. An garzaya da mamacin zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Rahoton ya ce an kama Saudat, kuma tana hannun rundunar CID a sashen da ke kula da laifukan kisan kai. Ana shirin gurfanar da ita a kotu bisa tuhumar aikata kisan kai.

Kwamishinan Ƴansanda, CP Bakori, ya jaddada cewa rundunar ba za ta yarda da aikata wani nau’in laifi a jihar ba, yana mai tabbatar da cewa za a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da adalci.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *