Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Rundunar Yansandan Najeriya reshen jihar Gombe ta tabbatar da kamawa da tsare wasu matasa biyu da ta ke zarginsu da aikata laifin fashi da makami a unguwar Nasarawo a birnin Gombe.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Ƴansandan jihar ASP Buhari Abdullahi, ya wallafa a shafin sa na Facebook ta ce, matasan masu suna Abubakar Musa mai shekara 22 da kuma
Usman Ismail ɗan shekara 20 an kama su da dauke da “Adda da Takobi in da suka farwa mutanen da ba su ji ba su gani ba, har ma su ka raba su da wasu daga cikin mahimman kayayyakinsu, da suka haɗa da wayoyin hannu wanda kimar kuɗinsu ta kai ɗubu dari shida da ɗaya”.
Me ganawar Gwamnan Gombe da Shugaban NNPCL ta ƙunsa?
Gwamnan Gombe Ya Sa Hannu Kan Takardar Yarjejeniyar Samar Da Tashar Wutar Lantarki A Jihar.
Yansandan Kano sun ƙuɓutar da yarinyar da matahi ya yi garkuwa da ita ya nemi kudin fansa miliyan 3.
Buhari Abdullahi ya ce da zarar Ƴansandan sun gama bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargin gaban kotu domin a yi musu hukunci.
Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su dinga kula tare da miƙa ƙorafinsu ga hukumar ƴansanda mafi kusa da su a kan lokaci.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Dokin rundunar Sojin Najeriya mai muƙamin Sajan ya mutu a Kaduna.
-
Ɓarawo ya mutu yayin da ya ke ƙoƙarin sata a cikin Taransifoma.
-
Yansadan jihar Adamawa sun fara bincike kan wasu mutum 2 da zargin sun yi wa yara mata biyu Fyade.
-
Yayin da Ƴansandan Kano su ka gargaɗi al’umma kan shiga cunkoso saboda barazanar tsaro gwamnatin jihar ta ce taron Mauludin Shehu Inyass ya na nan daram.
-
Wata gobarar tankar fetur ta ƙone direbanta a Ibadan.