Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yabawa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, bisa amfani da irin kuzari da jajircewar da ya nuna a Legas wajen inganta ci gaban Najeriya.
Macron ya yi wannan jawabi a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai da suka gudanar tare da Tinubu a Faransa, inda shugaban Najeriya ke ziyara tun daga ranar Laraba.
A yayin tattaunawar kan karfafa dangantaka tsakanin Faransa da Najeriya, Macron ya jinjinawa shugabancin Tinubu, musamman kan jajircewarsa wajen inganta tsaro a yankin ECOWAS.
Gwamnatin Najeriya za ta raba irin Alkama mai jure zafi ga manoma.
Sojan saman Nijeriya sun yi wa Ƴan Boko Haram fata-fata a Borno.
Kotu ta bayar da umarnin tsare Yahaya Bello bayan ya musanta zarge-zargen da ake masa.
Shugaban Faransa ya kuma jaddada yadda Tinubu ke karfafa kwarin gwiwa ga masu zuba jari daga Faransa da sauran kasashen duniya, wanda ke sanya Najeriya zama wurin da ya dace don zuba jari.
“Ina son taya ka murna kan shugabancinka da kuma burin da kake da shi na yin aiki tare da mu. Ina godiya gare ka, Shugaba, bisa wannan ziyarar kasashen waje. Ina godiya bisa kuzari da kwazonka.
“Bayan ka sauya jihar Legas, yanzu kana amfani da wannan kuzarin don sauya kasarka zuwa mafi kyau.
“Kuzarin da muka gani daga ministocin ka, masu zuba jari, da al’ummomin kasuwanci ya gamsar da mu kwarai a Faransa da kuma daukacin duniya don zuba jari a kasarka, sannan mu sanya Najeriya a matsayin babban abokin huldar yanzu da nan gaba,” inji Macron.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
“Kwararar masu aikata laifuka daga jihohin makwabta ne abin da ya taimaka wajen ƙalubalen tsaro”- Gwamnatin Gombe.
-
Kano da Katsina, sun zama a sahun gaba wajen matsalar rashin isassun takardun kuɗi.
-
Kamfanin Turkiyya zai fara haɓaka noman zamani a Zamfara.
-
Ƙungiyar Alkalai sun shiga yajin aikin sai baba ta gani.
-
NAFDAC ta gargaɗi masu gidajen Burodi kan amfani da Sakarin.