Yansanda Sun Tsare Mutumin Da Ya Caka Wa Ƴar shekara 8 Almakashi Da Cokali A Al’aurarta Har Sai Da Ta Sume.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Rundunar Ƴansandan jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya, ta tsare wani mutum mai shekara 32 bisa zargin caka wa wata yarinya mai shekara 8 almakashi a gabanta.

Mutumin ya yi wa yarinyar mummunan rauni a gabanta har sai da ta sume, a sakamakon wannan aika-aika da ya yi mata.

Aminiya ta rawaito, kakakin Ƴansanda na jihar, DSP Lawan Shi’isu Adam, ya ce jami’an tsaro sun kama mutumin ne bayan da ya yaudari yarinyar zuwa banɗaki a wani kamfanin sarrafa ruwan leda a garin Dutse, inda ya yi mata wannan ɗanyen aiki.

Biyan kudin fansa ba ya hana ƴan bindiga kashe wanda aka yi garkuwa da shi – Gwamna Radda.

Daga Ƙarshe Ɗan Ɗaban Da Ya Addabi Kano Abba Burakita Ya Mutu.

Ba ƙwace motocin sojoji ƴan bindiga su ka yi ba – Mazauna Zamfara.

Jami’in ya bayyana cewa mutumin ya sha cin zarafin yarinyar, kuma yana yi mata barazanar kashe ta da iyayenta, idan har ta kuskura ta sanar da wani.

DSP Lawal ya ce a halin yanzu mutumin yana tsare a hannun Sashen Binciken Manyan Laifuka  an ’Yan Sanda (SCID) da ke jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Proudly powered by WordPress | Theme : News Elementor by BlazeThemes