Tsohon gwamnan jihar Gombe, sanata Ibrahim Hassan Dankwambo da ke wakiltar mazaɓar Gombe ta arewa, ya buƙaci gwamnatin jihar da ta dakatar da biyansa kuɗin fansho na wata-wata da kimanin kudin ya kai Naira N700,000.
Dankwambo, a wata wasiƙa mai kwanan wata 4 ga Oktoba da ya aike wa gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya da LEADERSHIP ta samu a ranar Litinin, ya ce, biyansa fansho na wata-wata ya samu amincewa ne ƙarƙashin dokar mulki ta fansho na shekarar 2007.
A cewarsa, a kowane wata, gwamnatin jihar na biyansa kuɗin fansho da ya kai naira N694,557 a matsayinsa na tsohon gwamna, ya ƙara da cewa, biyo bayan shawarori da ya yi da ƙungiyoyin fararen hula, cibiyoyi, abokai da ‘yan uwa, ya amince da ya daina karɓan kuɗin fanshon.
“Don haka, na rubuta maka (Gwamna Inuwa) buƙatar ka dakatar da biyana fansho/alawus ɗin naira N694,557.82 da ake biyana a matsayin tsohon gwamnan jihar Gombe.”
Sanata Ibrahim, ya ƙara da cewa, tun lokacin da ya bar ofishin gwamnan jihar, ba ya samun cin gajiyar alawus-alawus da suka ƙunshi na kiwon lafiya, kuɗaɗen zirga-zirga da kuma na kwaskwarima ga kayan ɗaki.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi martani kan rahoton Amnesty.
-
An yi arangama tsakanin makiyaya da manoma a jihar Gombe.
-
Matuƙa Adaidaita Sahu za su dawo biyan haraji a Kano.
-
Emefiele ne ya mallaki unguwa mai gidaje 753 da EFCC ta ƙwace a Abuja.
-
Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kano ta tseratar da ran mutum 4 a cikin watan Nuwamba 3 sun rasu.