Kamfanin Dangote na tace man fetur ya sanar da wani sabon farashi na Premium Motor Spirit, wanda aka fi sani da fetur, daga Naira 865 zuwa Naira 835 a kowace lita.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an rage farashin ne bayan faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya, inda farashin ya sauka zuwa dala 64 a kowace ganga daya, daga fiye da dala 70 a cikin ‘yan makwannin da suka gabata.
Tsohon farashin da kamfanin ya saukar tun da farko daga naira 880 zuwa naira 865 a kowace lita, bai amfani masu amfani da fetur ba, domin ‘yan kasuwa ba su rage farashin ga jama’a ba.
Matatar Dangote wacce ke da karfin tace ganga dubu dari shidda da hamsin a kowace rana, na taka muhimmiyar rawa a tsarin makamashi na Najeriya.