Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta bayyana cewa hauhawar farashi a kasar ya ragu zuwa kashi 23.18% a shekara, daga watan Janairu zuwa Fabrairu 2025.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, NBS ta bayyana cewa raguwar hauhawar farashin ya biyo bayan sabunta ma’aunin Consumer Price Index (CPI) domin dacewa da sauye-sauyen yadda jama’a ke kashe kudin su.
Tun bayan sake daidaita ma’aunin a watan Disamba 2024, adadin hauhawar farashi ya sauka daga kashi 34.80 zuwa kashi 24.48 a watan Janairu 2025, wanda shi ne mafi girman raguwar hauhawar farashi da aka samu a cikin shekaru fiye da goma.
Hauhawar farashin abinci a watan Fabrairu 2025 ya tsaya a kashi 23.51 idan aka kwatanta da kashi 37.92 na Fabrairu watan 2024, wanda ke nuna raguwar kashi 14.41.
Sai dai a kididdigar wata-wata, hauhawar farashin abinci ya kasance kashi 1.67 a watan Fabrairu 2025, yayin da adadin hauhawar farashi ya tsaya a kashi 2.04 a wannan wata.