December 9, 2024

Ana Ci Gaba Da Shiga Da Gawarwaki Asibitin Gaza Bayan An Binne Gawa 179 A Cikin Sa.

Daraktan babban asibitin Gaza ya ce mutane dari da saba’in da tara, da suka hada da jarirai aka binne a wani ƙaton kabari da ke harabar asibitin.

BBC ta rawaito, Mohammad Abu Salmiyah ya ce majinyatan sun mutu ne bayan da kayan aikin asibiti masu muhimmanci suka gaza sakamakon katsewar wutar lantarki.

Ya ce jarirai bakwai da majinyata ashirin da tara na cikin waɗanda aka binne.

Salmiyah ya ce yanzu haka gawarwaki na cika asibitin sannan kuma babu wutar lantarki a dakin ajiyar gawa.

An bayar da rahoton tashin bama-bamai a kusa da kuma tankokin Isra’ila sun yi cunkoso a kofar asibitin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *