Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana samun karin kudaden shiga daga ma’aunin biyan kuɗi (Balance of Payments BOP), har dala biliyan 6.83 a shekarar 2024, wanda ke nuna sauyin al’amurra daga gibin dala biliyan 3.34 da aka samu a 2023 da kuma dala biliyan 3.32 a 2022, bisa ga wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Laraba.
“Wannan ci gaba yana nuna tasirin sauye-sauyen tattalin arziki na kasa baki daya, da kyakkyawan sakamakon cinikayya, da sabuwar kwarin gwiwar masu zuba jari a tattalin arzikin Najeriya,” in ji babban bankin.
CBN ya bayyana cewa current account capital account na kasa sun samu karin dala biliyan 17.22 a 2024, wanda cinikin kaya ya taimaka da dala biliyan 13.17. Shigo da kayayyakin mai sun ragu da kashi 23.2 zuwa dala biliyan 14.06, yayin da shigo da kayan da ba na mai ba suka ragu da kashi 12.6 zuwa dala biliyan 25.74.
A bangaren fitar da kayayyaki, fitar da iskar gas ta karu da kashi 48.3 zuwa dala biliyan 8.66, sannan fitar da kayan da ba na mai ba ya karu da kashi 24.6 zuwa dala biliyan 7.46. Shigowar kuɗaɗen da ‘yan Najeriya ke turawa daga ƙasashen waje ya ci gaba da kasancewa, inda tura kuɗin kai tsaye ya karu da kashi 8.9 zuwa dala biliyan 20.93.
A cewar CBN, shigowar kuɗaɗen da aka turo ta hanyar International Money Transfer Operators (IMTO) sun karu da kashi 43.5 zuwa dala biliyan 4.73 daga dala biliyan 3.30 a 2023, alamar karin hulɗa daga ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya