Labarai
Trending

Cacar Baka: Wani Mutum Ya Harbe Abokinsa A Jihar Adamawa.

Daga Firdausi Ibrahim Bakondi

A jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, Rundunar ‘yan sandan jihar ta kama wani mutum mai suna Wawe Nokomari mai shekaru 45 bisa zargin da ake masa na harbin abokinsa Mai suna Ham Musa.

Lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Nuwamba a unguwar Jabi da ke karamar hukumar Shelleng, inda wanda abin ya shafa ya samu munanan raunuka.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ake zargin mahaifin ‘ya’ya takwas ne, ana zargin cewa yasha kayan maye ne wato “burkutu” inda cacar baka ta haɗa su da abokin nasa da suke aiki a gonar shinkafa, sanadin haka ya bude masa wuta.

Daily Trust ta rawaito, mutanen biyu, wadanda aka ce dukkansu sun bugu ne, sun samu rashin fahimta ne wanda ya yi sanadiyar harbin.

Wata majiya na cewa Nokomari ya ari bindigar da ya harbi abokinsa da ita ne daga hannun wani dan banga.

A halin yanzu dai wanda aka harba din yana samun kulawa kuma an bayyana cewa yana cikin koshin lafiya.

Kazalika kwamishinan ‘yan sandan jihar, Afolabi Babatola, ya umarci sashin binciken manyan laifukan a ƴan sanda da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Nguroje ya kuma bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan ya bayar da umarnin kama dan bangar wanda ya ba da aron bindigarsa ga wanda ake zargin.

Rundunar ‘yan sandan ta sha alwashin tabbatar da cewa an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya, sannan ta bukaci jama’a da su sanya ido tare da kai rahoto ga jami’an tsaro a duk lokacin da suka ga wani abinda ba su gamsu dashi ba.

Wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ya nuna nadamar abin da ya aikata, ya kuma yi alkawarin kauracewa shan barasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button