Labarai
Trending

Najeriya Ita Ce Fitilar Da Ke Haskaka Afrika- Tinibu.

Daga Firdausi Ibrahim Bakondi

A daren ranar litinin din da ta gabata ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya, ya ci gaba da tattaunawa game da samar da kuɗaɗen da za’a samar da ababen more rayuwa na biliyoyin daloli daga Bankin Raya Musulunci don tallafawa manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa a matakin tarayya da na kasa da kasa a Najeriya a garin Makka na Saudiyya.

Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Ajuri Ngelale, shine ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce ci gaban da aka samu ya kasance ne sakamakon tattaunawa mai mahimmanci na zuba jari da aka gudanar tsakanin shugaba Tinubu da mataimakin shugaban bankin ci gaban Musulunci, Dokta Mansur Muhtar, bayan dawowar shugaban daga Sallar Magaruba.

Hukumar ta IDB ta bayyana cewa bankin ya sanar da samar da dala biliyan 50 na sabon saka hannun jari ga nahiyar Afirka daga kungiyar haɗin gwiwar Larabawa (ACG).

Sanarwar ta kara da cewa Tinubu ya ce, “Najeriya ita ce fitilar da ke haskaka hanyar Afirka baki daya, yace kuma da zarar Afirka ta haskaka, duniya za ta kasance wuri mafi haske ga daukacin al’umma, ya kuma ce ya kuduri aniyar samar kyakkyawar rayuwa ga matasa masu hazaƙa.

Ya ci gaba da cewa zuba jari a Najeriya zai kasance cikin mafi yawan samar da kayayyaki masu inganci a fadin duniya, ya ƙara da cewa masu saka hannun jari za su samu ci gaba cikin sauƙi a ciki da wajen ƙasar Najeriya, wanda tsarin zai zama abin koyi.

Yace bankin Musuluncin zai zama abokin tarayya wajen samar da ababen ci gaba.

Ya jaddada irin gibi da ake dashi a cikin ababen more rayuwa wanda suka haɗa da tashar jiragen ruwa, samar da wutar lantarki, da kayan aikin noma da za su ba da damar dorewar abinci a Najeriya, ya ce waɗannan kalubale suna ba da dama mara ƙima ga masu saka hannun jari a cikin kasuwar da ta fi girma a nahiyar.

Yace muna da hangen nesa don ba da damar inganta tafkin Lekki kafin lokaci ya kure.

Yace dole ne mu sake yin ƙarfin hali don mun gaji manyan lamuni, wanda za su bamu damar samun nasara.

Tinubu yace Akwai sassa da yawa da ke cike da damar saka hannun jari ga masu son saka hannun jari, yana mai cewa samun isassun kuɗade na iya zama cikas a wasu lokuta.

Ya ƙara da cewa muna ganin ku a matsayin abokan shawari da kuma na tafiya, kamar yadda kukayi tarayya da mu a baya, muna son haɓaka shi a yanzu don muyi abubuwa da yawa tare da babban buri da hangen nesa.

Shima a nasa bangare mataimakin shugaban bankin ya bayyana wa shugaba Tinubu cewa, la’akari da tarihi da kuma sauye sauyen tattalin arziki na shugaba Tinubu, ya yanke hukuncin sanya Najeriya cikin hada hadar kasuwanci, wanda yace duniyar hada-hadar kudi tana sa ido kan abubuwan da suka faru a Najeriya kuma ta kammala cewa mafi girman tattalin arzikin Afirka na nufin kasuwanci a kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button