Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Zuwa yanzu cutar Kyandar Biri na ƙara ɓarkewa a Najeriya in da ta yaɗu zuwa wasu jihohi 19 na ƙasar da kuma babban birnin tarayya Abuja in da ta kama mutum 40.
Daily Trust ta rawaito, a wani rahoto daga cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ya kuma nuna cewa kawo yanzu akwai jimillar mutane 802 da ake zargin sun kamu da cutar a jihohi 33 na tarayyar kasar.
An fitar da wannan rahoton halin da ake ciki kwanaki kadan kafin gwamnatin Amurka ta ba Najeriya gudummawar alluran rigakafin cutar guda 10,000.
Sabbin alƙaluman da aka samu daga NCDC sun nuna cewa an tabbatar da bullar cutar guda 40 a Najeriya tun a ranar 19 ga wannan wata, wanda ya kasance farkon mako na 34 na shekarar 2024.
Kawo yanzu dai ba a sami rahoton mutuwa daga cutar ba cikin kasar a bana.
Jihohin da aka tabbatar sun kamu da cutar sun hada da Bayelsa (5) Akwa Ibom, Enugu, Cross River (4 kowannensu), Benue (3), Babban Birnin Tarayya (FCT), Delta, Anambra, Rivers, Plateau (2 kowanne) Nasarawa, Legas, Zamfara, Kebbi, Oyo, Abia, Imo, Ebonyi (1 kowanne) da Osun (2).
APCin Kano Na Son EFCC Ta Yi Bincike Kan Bidiyon Ɗan Bello.
Ya zuwa yanzu, an tabbatar da bullar cutar guda 2,863 da kuma mutuwar mutane 517 a cikin kasashen Afirka 13 a cikin wannan shekarar kaɗai.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki A Jihar Zamfara.
-
Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Ayyana Ƙasar Masar A Matsayin Wadda Ta Kawar Da Sauro.
-
Cutar Sanƙarau Ta Kashe Mutum 85 A Jihar Yobe, Inda Hukumomi A Suka Ƙaryata Mutuwar Sama Da Yara 200.
-
Cutar Kyanda Ta Kashe Ƙananan Yara 19 A Jihar Adamawa.