Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun kama Sirajo Jaja, Akanta Janar na jihar Bauchi bisa zargin almundahanar Naira biliyan saba’in.
An kama shi a Abuja a ranar Laraba 19 ga watan Maris 2025, tare da Aliyu Abubakar na Jasfad Resources Enterprise, wanda ke gudanar da harkar canjin kudi ba tare da lasisi ba, da kuma Sunusi Ibrahim Sambo wanda ke sana’ar POS.
An kama su ne dangane da binciken da EFCC ke yi kan zargin almundahanar kudi, da karkatar da kudaden jama’a da kuma barnatar da dukiyar gwamnati da suka kai har Naira biliyan 70.
Hukumar tana kuma binciken Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, dangane da lamarin.
EFCC ta ce bincike ya nuna cewa an cire kudi har Naira biliyan 59 daga asusun banki daban-daban, da Akanta Janar din ya bude kuma yake tafiyarwa a madadin gwamnatin jihar.
Ana zargin cewa kudaden an tura su zuwa ga Abubakar da Sambo, wadanda kuma suka rarraba kudin ga wakilan jam’iyya da abokan siyasar gwamnan.
Ana kuma zargin cewa Abubakar wanda ke gudanar da canjin kudi, ya samu beli a baya, amma yanzu an sake cafke shi.
Tashar talabijin ta Channels ta ruwaito cewa, Kakakin EFCC Dele Oyewale, ya tabbatar da kama mutanen.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya