Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar Kano kuma Shugaban Kwamitin Kula da Ayyuka na jihar (SSC) na aikin KANO-ACReSAL, dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya kai ziyarar duba aiki wajen da ake gudanar da aikin tantancewa, tabbatarwa, da rajistar mutanen da aikin zai shafa (PAPs) a unguwar Bulbula-Gayawa.
A cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba 16 ga watab Afrilu 2025, ziyarar na daya daga cikin matakan da ake dauka domin tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen aiwatar da aikin dakile zaizayar kasa a yankin Bulbula-Gayawa da ke karamar hukumar Nasarawa.
Kwamishinan ya samu rakkiyar Kwamishinan filaye da Tsare-tsaren Birane Hon. Abduljabbar Umar, da takwaran sa daga Ma’aikatar Ayyuka, Injiniya Marwan Ahmad, tare da wakilan kamfanin da ke gudanar da aikin.
Yayin ziyarar dakta Dahiru ya zagaya da tawagar a yankin da aka tsara gudanar da aikin, inda ya yi musu bayani kan yadda aikin zai kasance tare da tattaunawa da mazauna yankin da aikin zai shafa.
Aikin tantancewar na nufin tabbatar da sahihancin mutanen da aikin zai shafa da kuma korafe-korafen su, domin tabbatar da biyan diyya yadda ya kamata da kuma samun saukin aiwatar da matakan dakile zai zayar kasa.
Kwamishinan ya kara jaddada kudirin gwamnatin jihar na kare muhalli da inganta rayuwar al’umma, ta hanyar aiwatar da ayukka cikin gaskiya da hadin kai karkashin shirin KANO-ACReSAL.