Labarai
Trending

Gwamnatin Kano Za Ta Kwato Gine-gine Da Filayen Dutsen Dala Da Wasu Suka Mallakawa Kansu.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

A jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, sabon babban sakataren Ma’aikatar Kula da Tarihi da Al’adu ta jihar ya ce, da zuwan sa ma’aikatar ya tarar da ita, da sauran bangarorinta tamkar Makabarta saboda rashin kulawa na gwamnatin da ta gabata.

Ahamd Abba Yusuf, shine Sakataren ya bayyana hakan ne cikin wani shirin kai tsaye da Martaba FM Online ta yi da shi a shafinta na Facebook a farkon makon nan.

https://www.facebook.com/martabafm/videos/1291219894906877/?mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

Babban sakataren ya ce ko a lokacin da aka tura shi ma’aikatar domin aikin Sakatare ya ji ana ta faɗin wai-wai gurin sai mara gata ko mara galilhu ake turawa, domin ana kira gurin tamkar Makabarta, “na zo na tarar da wannan ma`aikata da sauran bangarori daban-daban na ta a cikin wani hali da za a iya cewa na ha`ula`I, ana ma kiran wajen kamar Makabarta nima na tabbatar da haka, irin halin ko in kula da gwamnatin baya ta nunawa wannan muhimmin fanni”.

Ya ƙara da cewa babban abincin takaicin shine yadda ma’aikatan gurin ke jayayya kan shiga hurumin aiki, saboda haka ne suka duƙufa, wajen ganin an tsara aikin ta yadda kowa zai fahimci aikin sa, inda ya ce hatta da ƙudiri da burukan ma’aikatar sai da suka zo suka tattara su, suka kuma buga su, ta yadda duk wanda ya kai ziyara ma’aikatar zai fahimci aikin su.

Sakataren ya ce sun zagaya gurare da dama na tarihi amma sun tarar da su babu wani ci gaba, wanda ya ce ko da suka je Dutsen Dala sun tarar gurin ya zama mafakar bata gari, da tarin ƙazanta, acewarsa hatta ofisoshi na ma’aikatar da ke Dutsen Dala da ma sassan katanga da jikin Dutsen wasu mutane mazauna kewayen Dutsen sun mallakawa kansu, inda ya kuma yi zargin gwamnatin baya ta mallakawa wasu, to amma ya ce akwai yiwuwar gwamnatin Kano ƙarƙashin gwamnatin Abba Kabir Yusuf, zata kwato guraren.

Ya sha alwashi kawo sauyi ta hanyar yin manyan gyare-gyare da za su bunƙasa kuma al’ummar jihar Kano su fahimci aikin ma’aikatar sosai, wanda hakan zai zama hanyar bunƙasa taltalin arziki jihar, da kuma kawo ci gaba, da yanayi mai kyau domin karɓar baƙi masu yawon buɗe ido da kuma masu bincike ko son sanin ilimin tahiri, da al’adu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button