Labarai
Trending

Gwamnatin Neja Ta Janye Dakatar Da Haƙar Ma’adinai A Jihar.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Gwamnatin jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya, ta dage dakatarwar da ta yi wa duk wasu masu ayyukan hakar ma’adinai a faɗin jihar.

Mukaddashin gwamnan jihar, Yakubu Garba ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin yaƙi da hako ma’adinai da lalata muhalli ba bisa ƙa’ida ba a jihar.

A cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Bologi Ibrahim ya fitar, ta ce muƙaddashin gwamnan ya lura cewa harkar ma’adanai na da matukar muhimmanci wajen bunƙasar tattalin arziki, in da ya nuna takaicin yadda ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba ke yin illa ga muhalli a jihar, kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.

Ya bayyana cewa daga cikin bayanan da ake da su, akwai kamfanonin hakar ma’adinai 880 da suka yi rajista wadanda suka hada da kamfanoni 578 da kuma kungiyoyin hadin gwiwa 302 a jihar.

Ya ce, duk da haka, kusan kamfanoni 261 ne kawai su ka zo dan tantancewa.

Ambaliya: Mutum Kusan 50 Sun Rasu In Da Dubbai Suka Rasa Muhallansu A Najeriya.

Iyalan Sarkin Kano Ado Sun Ƙaryata Alaƙa Da Zainab Wadda Take Iƙrarin Ita Ɗiyar Sarkin ce.

Yakubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa rundunar musamman da aka kafa za ta aiwatar da ka’idoji tare da tabbatar da ayyukan hakar ma’adinai akan doron doka da tsare-tsaren gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button