April 18, 2025

Hukumar Jin Dadin Alhazzai ta jihar Niger ta fara rarraba unifom da wasu kayayyaki ga mahajjata

Hukumar Jin Dadin Alhazzai ta jihar Niger ta fara rarraba unifom da kuma karamar jakka mai nauyin kilo 8 ga mahajjata masu niyyar zuwa hajjin bana, a matsayin wani bangare na shirye-shiryen Hajjin shekarar 2025 a Saudiyya.

A jawabin sa yayin rarraba kayan, Sakataren zartarwa na hukumar Sheikh Muhammad Awwal Aliyu, ya bayyana cewa wannan rarraba kayan mataki ne mai muhimmanci don tabbatar da tafiyar da aikin hajji cikin sauki, da rashin samun tangarda ga mahajjatan jihar Niger.

Sakataren zartarwar wanda Daraktan mulki Babani Aliyu Yahaya ya wakilta, yayin da yake mikawa jami’in kula da jin dadin mahajjata na karamar hukumar Chanchaga da kuma shugaban jami’an kula da mahajjata na kananan hukumomi (APWO) a jihar, ya ce unifom da jakar hannu mai kilo 8 mallakar mahajjatan ne, da suka kammala biyan kudin su.

A cewar sa, jakar hannu mai kilo 8 da aka bai wa jami’an kula da mahajjata a matakin karamar hukuma (APWO) an tanadar da ita ne, domin taimakawa wajen tafiyar da kayan mahajjata yadda ya kamata da kuma saukaka musu tafiya.

A nasa jawabin bayan karbar unifom da jaka mai kilo 8 ga mahajjatan karamar hukumar Chanchaga da kuma matsayin sa na shugaban APWO Alhaji Abu Sufyanu, ya yi alkawarin raba kayan yadda ya dace ga mahajjatan, tare da tabbatar da cewa zai tsaya tsayin daka, wajen ba da ingantacciyar hidima yayin da suke shirye-shiryen taimakawa mahajjata wajen gudanar da tafiyar su ta ibada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *