Labarai
Trending

Hukumar Tace Fina-finai Ta Wanke Maryam Yahaya Daga Zargin Bidiyon Rungume-rungume.

Daga Zainab Adam Alaramma

Hukumar tace fina-fina da daf’i ta jihar Kano ta wanke Jarumar masana’antar Kannywood Maryam Yahaya bisa wani zargi da akai mata na rungumar wani saurayi a cikin wani bidiyo.

Abdullahi Sani Sulaiman, wanda shine Mai magana da yawun hukumar ne ya bayyana hakan ga freedom Radio

Ya ce, an kai musu korafi akan jaruma Maryam Yahaya kan wani bidiyo da ake yadawa a kafafen Sada Zumunta, Inda aka ga wani yana rungumar wata wacce ake zargin Maryam Yahaya ce, amma sun gudanar da bincike sun gano cewa ba Maryam Yahaya ba ce a cikin bidiyon.

Abdullahi Sani Sulaiman ya ƙara da cewa, shugaban hukumar tace fina-fina ta jihar kano Abba El-Mustapha ya baiwa daraktan dake kula da Yan masana’antar Kannywood damar gudanar da bincike don tabbatar da anyi adalci ga kowanne bangare.

Binciken dai ya wanke Maryam Yahaya saƙal, inda ya ce, bayan kammala binciken hukumar sun ta tabbatar da cewa Wacce ake zargin ba jaruma Maryam Yahaya ba ce, don haka suka ga dacewar su fito su shaidawa duniya cewa ba Maryam bace, saboda abun ya yadu da yawa bai dace su yi shuru akan maganar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button