March 12, 2025

Kotu a jihar Akwa Ibom ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun sa da laifin kisan kai.

Wata babbar kotu a jihar Akwa Ibom da ke zaman ta a Abak ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Eno Isangidihi, ta yanke wa wani mutum mai suna Akaninyene Johnson Nkonduok hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon laifin kisan kai.

Lamarin da ya kai ga wannan hukuncin ya faru ne a shekarar 2021, a kauyen Utu Ikot Imonte da ke ƙaramar hukumar mulkin Etim Ekpo a jihar.

A cikin bayanin shari’ar mai lamba HA/35C/2021, an bayyana cewa mai shela na kauyen mai suna Imoh Amos bisa umarnin shugabannin garin, ya sanar da wajibcin yin aikin tsaftace muhalli a ƙauyen a washegari.

Bisa tsarin ƙauyen ana buƙatar duk matasa su halarta, kuma duk wanda ya ki halarta zai biya tarar da aka kayyade.

A cewar lauyar gwamnati da ke gabatar da ƙara Mrs. Nancy Idungafa, ta ce mai shela tare da wasu mutanen ƙauyen sun tafi wurin wanda ake tuhuma domin jin dalilin da yasa bai halarci aikin tsaftar muhallin ba.

Kotu ta ji cewa wanda ake tuhuma ya fusata, ya ɗauko adduna, ya kaiwa Amos farmaki in da ya ji masa raunuka, wanda hakan ya haddasa mutuwar sa.

Nan take aka kama shi, kuma daga ƙarshe aka gurfanar da shi a babbar kotun.

Bayan doguwar shari’a da lauyan sa Utibe Nwoko ya yi ƙoƙarin kare shi, kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *