Labarai
Trending

Kuɗin Cizo Ya Addabi Al'ummar Koriya Ta Kudu.

Hukumomin Koriya ta Kudu suna aiki ba ji-ba gani don shawo kan bullar kudin cizo da ya janyo damuwa a fadin kasar.

An samu bullar kwaron mai shan jini a sassan babban birnin Seoul 17, da biranen Busan da Incheon ya zuwa ranar 5 ga wannan wata na Nuwamba, a cewar kafofin yada labaran kasar.

Birnin Seoul ya ware kudin kasar won miliyan 500 kwatankwacin naira miliyan 380 a canjin hukuma tare da kafa kwamitin kai dauki ga annobar kudin cizo.

Wannan kwaro ya kuma zama wani batun fargaba a tsakanin jama’a cikin ‘yan kwanakin baya-bayan nan a Faransa da kuma Birtaniya.

Tun a watan Satumba ne aka ba da rahoton bullar kudin cizo a Koriya ta Kudu, a wata jami’a da ke birnin Daegu na kudu maso yamma. Daga bisani an ba da rahoton ganin kudin cizon a dakunan masu yawon bude ido da gidajen wankan hutu.

Wasu ‘yan Koriya ta Kudu sun rika gujewa shiga silima da ababen hawa na jama’a saboda fargabar diban kudin cizo.

Mun bayyana samu wannan labarin daga BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button