Labarai

Ƴan Bindiga sun harbi wani dalibin jami’a tare da sace dan kasuwa a Nassarawa

Yan bindigar dauke da muggan makamai sun kutsa yankin da misalin karfe 8:30 na dare

Wasu ’yan bindiga sun kai farmaki unguwar Gandu da ke kusa da Jami’ar Tarayya ta Lafia a Jihar Nasarawa, inda suka sace wani dan kasuwa tare da harbi wani dalibi guda daya.

’Yan bindigar dauke da muggan makamai sun kutsa yankin da misalin karfe 8:30 na dare suna harbi don tsorata al’ummar yankin da kewaye.

Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar da har yanzu ba a tantance ko su wane ne ba sun yi garkuwa da wani dan kasuwa inda suka tafi da shi wurin da ba a sani ba.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa daliban da ke zaune a unguwar Gandu sun zauna a gida tun karfe 7 na dare saboda fargabar harin ’yan bindigar.

Wani dalibi a ajin karshe na Jami’ar, a Sashen ‘Biochemistry’ wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa ya ce a kwanakin baya, mahara sun tare dalibai sannan suka kwace musu wayoyi.

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar, ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a manyan makarantun jihar.

Ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kai wa Shugaban Jami’ar Tarayya ta Lafia kan harin da ’yan bindiga suka kai wa dalibai a daren ranar Litinin.

Gwamna Sule ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta inganta tsaro ga daliban domin dakile matsalar tsaro.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Shehu Abdulrahman ya nemi gwamnatin jihar ta samar da ofishin ’yan sanda a yankin da domin tabbatar da tsaron daliban.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button