Daga Abdul’aziz Abdullahi
Majalisar tsaro ta jihar Gombe ta yi ganawar gaggawa domin shawo kan matsalar tsaro tsakanin makiyaya da manoma tare da masu satar Shanu da su ka addabi wasu yankunan jihar.
A yayin tattaunawar wadda mataimakin gwamnan jihar Manasseh Daniel Jatau, ya jagoranta ranar Litinin, majalisar ta sha alwashin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Gombe wacce ta kasance jiha mafi zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.
Majalisar ta amince da ƙara tsaurara matakan tsaro domin kawo ƙarshen barazanar tsaron, sannan ta buƙaci al’umma da su sanya ido tare da kai koken duk wani motsin da ba su aminta da shi ba.
An yi arangama tsakanin makiyaya da manoma a jihar Gombe.
Ƴansandan jihar Gombe sun kama wasu matasa biyu bisa zargin fashi da makami.
Me ganawar Gwamnan Gombe da Shugaban NNPCL ta ƙunsa?
Gwamnatin ta kuma bayyana kwararar masu aikata laifuka daga jihohin makwabta a matsayin abin da ya taimaka wajen ƙalubalen tsaron.
Taron ya samu halartar SSG, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, kwamishinoni da abin ya shafa, shugabannin hukumomin tsaro, shugabannin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.
-
Gwamnan Kano ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Ma’aikatar Bibiya da tabbatar da Nagartar Aiki.
-
Gwamna Zulum zai saka tallafin man fetur ga manoman yankin da rikicin Boka Haram ya shafa.
-
Sarakunan da Fintiri ya naɗa bayan ƙirƙirar masarautu 7 a jihar Adamawa.