Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama wani adadin kuɗi har dala dubu dari daya da tas’in da ukku (kimanin Naira biliyan 289 da miliyan dari biyar), da aka boye a cikin katon ɗin yoghurt a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Kakakin hukumar Abdullahi Maiwada, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Abuja, inda ya bayyana cewa an kama kuɗin ne a ranar Alhamis.
Ya ce wanda ake zargin yana cikin jirgin Ethiopian Airlines mai lamba 951 daga Jeddah ta kasar Saudiyya.
Maiwada ya bayyana cewa an gudanar da wannan aiki ne bisa sahihan bayanan sirri, da kuma cikakken binciken kaya na wani fasinja da ke shigowa ƙasar.
“Bisa bayanan sirri, jami’an Kwastam sun gudanar da bincike na musamman, wanda ya kai ga gano kuɗin da aka ɓoye,” in ji shi.
Ya bayyana cewa waɗannan kuɗaɗen da ba a bayyana ba sun saɓa wa dokar Kuɗi (Prevention and Prohibition) ta 2022 da Dokar Hukumar Kwastam ta 2023.
Waɗannan dokoki sun tanadi cewa duk matafiyi da ke ɗauke da fiye da dala dubu goma ($10,000) ko makamancin hakan, dole ne ya bayyana wa Hukumar Kwastam lokacin shigowa ko ficewa daga ƙasar.
Maiwada ya ce fasahar bincike ta zamani ta taimaka wajen gano nauyin da bai dace ba a cikin kayan wanda ake zargi.
Ya ce “An miƙa kuɗin da aka kwace ga Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar gurfanarwa a gaban kotu.
“Kamar yadda doka ta tanada, muna miƙa kuɗaɗen da aka ƙwace ga hukumar EFCC domin ci gaba da daukar matakan da suka dace,” in ji shi.
Ya sake jaddada kudirin Hukumar Kwastam na tabbatar da bin ka’idojin kuɗi, da kuma hana zirga-zirgar haramtattun kuɗaɗe ta iyakokin ƙasa.
Har ila yau, ya shawarci matafiya da su kiyaye doka ta hanyar bayyana duk wani kuɗi ko takardun kuɗi masu amfani da suka wuce iyakar da aka kayyade yayin shigowa ko barin Najeriya.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya