A jihar Bauchi Majalisar Masarautar Bauchi ta janye soke hawan Sallah da ta yi a baya, ta na mai sanar da yin hawan na shekarar 2025
Tin da farko cikin wata sanawa da ta fitar a ranar Juma’a mai ɗauke da sa hannun sakataren masarautar Bauchi Alhaji Shehu Mudi Muhammad, ta ce Kwamitin Shirya Daba na masarautar ya soke hawan, kuma ya nemi amincewar gwamanti jihar, in da gwamnatin ta amince da soke hawan na bana.
To amma cikin sabuwar sanarwar da ta fitar masarautar ta ce hawan ya na nan za a yi “Majalisar Masarautar Bauchi ta na farin cikin sanar da jama’a cewa yanzu za’a gudanar da bukukuwan Hawan Sallah na shekarar 2025 kamar yadda aka tsara. Bayan nazari da tuntubar gwamnatin jihar Bauchi, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya amince da ci gaba da gudanar da wannan gagarumin biki.”
“Bikin Sallah wani muhimmin bangare ne na al’adunmu, kuma muna farin ciki tare da marhabin da mazauna, maziyarta, da masu yawon bude ido don halartar bukukuwan sallar bana”, in ji sanarwar.
Masarautar ta ce nan gaba za ta sanar da cikakken bayanai game da jadawali da shirye-shiryen hawan ba da jimawa ba.