Labarai
Trending

Masarautar Bauchi Ta Tuɓe Rawanin Masu Sarautar Gargajiya 6.

Daga Firdausi Ibrahim Bakondi

Majalisar Masarautar Bauchi ta kori wasu masu rike da sarautar gargajiya guda shida a gundumar Galambi ƙaramar hukumar Bauchi da ke jihar.

Cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na masarautar, Babangida Hassan Jahun, ta bayyana cewa an yanke hukuncin ne sakamakon saɓawa ka’idoji da hakimin na Galambi yayi.

Daily Trustta rawaito, a ranar Lahadin da ta gabata cewa Hakimin Galambi, Alhaji Shehu Adamu Jumba, mai rike da sarautar Danlawal na Masarautar Bauchi a kwanan baya ya nada wasu mutane shida a fadarsa wanda suka hada da, Galadaman Danlawal, Wakilin Dokan Danlawal, Majidadin Danlawal, Wakilin Gonan Danlawal, Sarkin Dajin Danlawal da Hardon Danlawal.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, majalisar masarautar ta kuma haramta wa Hakimin gudanar da irin wannan naɗin na tsawon shekara guda wanda ya fara daga ranar 7 ga watan Nuwamba, inda ta ce, Dole ne a ko da yaushe ya tabbatar da cewa duk wani aikin rawani dole ne ya kasance daidai da ka’idojin da aka shimfida a cikin babbar masarautar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button