Labarai
Trending

Jami'in Tsaron Najeriya Sun Kama Waɗanda Kaiwa Shugaban Kungiyar Kwadago Hari.

Daga Firdausi Ibrahim Bakondi

A ranar Laraba ne mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya nemi afuwar kungiyar kwadago kan harin da aka kai wa shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, a Owerri, babban birnin jihar Imo, a ranar 1 ga watan Nuwamba.

Ajaero, wanda ya kai farmaki garin Owerri domin jagorantar zanga-zangar, an yi masa mugun duka tare da tsare shi na wasu sa’o’i.

A Sakamakon haka ne, ma’aikata suka baiwa gwamnati wa’adin biyan wasu bukatu da suka haɗa da kama wadanda suka kai harin Ajaero, tare da yin barazanar fara yajin aikin a fadin kasar idan ba a biya musu bukatun su ba.

Gwamnatin tarayya dai ta garzaya kotu domin hana ma’aikata shiga yajin aiki, amma yajin aikin ya fara a ranar Litinin, wanda ya gurgunta al’amura da dama a fadin kasa.

A wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Zakari U Mijinyawa ya sanyawa hannu a ranar Talatar da ta gabata, Ribadu ya bukaci kungiyar da ta janye matakin da ta dauƙa na shiga yajin aikin da take ci gaba da yi a yanzu haka, inda ya kara da cewa an kama wadanda suka kai hari wa Ajaero, kuma tuni aka fara bincike a kansu.

Ribadu ya ce gwamnatin tarayya ta yi nadamar abin da ya faru a Imo, kuma ta yi Allah wadai da shi , yana mai cewa hakan ya saɓa wa doka da ka’idojin ‘yancin faɗin albarkacin baki da Shugaba Tinubu da gwamnatinsa suka bi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button