April 18, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Masu garkuwa da mutane sun nemi kuɗin fansa na Naira miliyan 100 domin sakin Fasto a jihar Kaduna.

Masu garkuwa da mutane sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 100 domin sakin Fasto Samson Ndah Ali, wani malamin coci mai shekara 30 da ke cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) a Mararaba Aboro, karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna.

An sace faston ne daga gidan sa da safiyar Litinin da misalin karfe ɗaya na dare, inda wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka shiga gidan sa tare da tafiya da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, sakataren kudi na cocin mista Yusuf Ambi, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, ya kasance tare da faston a daren kafin abin ya faru, sai kawai ya samu kiran gaggawa da safiyar Litinin.

“Na garzaya gidan sa inda yake zama shi kadai, amma na iske kofa a bude, na duba duk dakunan, amma ban same shi ba,” in ji shi.

Ambi ya kara da cewa daga baya masu garkuwa da mutane sun tuntube su, inda suka nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa don sakin faston.

Ya ce suna kan tattaunawa da su akan hakan.

Ya bayyana cewa Fasto Ali, wanda dan asalin kauyen Danji ne a Ungwan Mailafiya, bai jima da fara aiki a cocin ba, kasa da makwanni biyu kafin sace shi.

Hadin gwiwar jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, da kuma jami’an hukumar DSS sun kaddamar da wani samame don ceto faston da aka sace.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna DSP Mansir Hassan, ya yi alkawarin mayar da martani kan lamarin, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai yi hakan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *