April 18, 2025

Sabon harin Isra’ila a Gaza ya yi ajalin mutum 35 tare da jikkata wasu 55.

Harin da Isra’ila ta kai sau da dama kan gine-gine a unguwar Shujayea na birnin Gaza, ya hallaka akalla Falasɗinawa 35 tare da jikkata wasu 55, yayin da mutane 80 ke ci gaba da ɓacewa a ƙarƙashin baraguzan gine-ginen da aka rushe.

Aljazeera ta ruwaito cewa waɗanda suka shaida harin sun ce “kisan kare dangi ne da cikakken ma’anar kalmar,” yayin da wata asibiti da ke cikin cunkoso ta roƙi gudunmawar jinin agaji domin ceto rayukkan waɗanda suka samu munanan raunuka.

Dakarun Isra’ila sun gudanar da wani gagarumin samame a sansanin ‘yan gudun hijira na Balata, da kuma kusa da garin Nablus a yankin West Bank da Isra’ila ke mamaya.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce akalla Falasɗinawa dubu hamsin da dari takwas da arba’in da shidda ne aka tabbatar da mutuwar su tare da jikkata dubu dari daya da goma sha biyar, da dari bakwai da ashirin da tara sakamakon yaƙin Isra’ila da Gaza.

Ofishin Yaɗa Labarai na Gwamnati ya sabunta alkaluman mutuwar zuwa sama da 61,700, yana mai cewa dubban da suka ɓace a ƙarƙashin baraguzan gine-gine ana kyautata zaton sun mutu.

Akalla mutane 1,139 ne aka kashe a Isra’ila a yayin hare-haren da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba 2023, tare da fiye da mutane 200 da aka sace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *