Kungiyar Matasa ta Sahel masu rajin samar da Kyakkyawan jagoranci da Wayar da Kan Jama’a, ta yi Allah wadai da matakin Shugaba Bola Ahmad Tinubu na ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers, ta na mai bayyana hakan a matsayin matakin da ya wuce gona da iri, kuma barazana ga dimokuradiyya da ‘yancin jama’a.
A cikin wata sanarwa da shugaban ta Comrade Aminu Harsanu Guyaba ya sanya wa hannu, kungiyar ta soki matakin tana mai cewa hakan cin fuska ne ga tafiyar da mulkin dimokuradiyya, kuma yana haifar da shakku game da hakikanin manufar sa. Kungiyar ta yi gargadi cewa irin wadannan matakai a tarihi, kan haifar da rashin amincewa da shugabanni da kuma gurbata harkokin gwamnati.
Sanarwar ta kuma yi nuni da mulkin tsohon Gwamna Nyesom Wike, wanda ta bayyana a matsayin mai cike da cece-kuce da kuma barazana ga dimokuradiyyar Najeriya. Kungiyar ta zargi Wike da yin amfani da karfin mulki don murkushe ‘yan adawa, tana mai fargabar cewa dokar ta-baci na iya kara dagula siyasar jihar Rivers.
Duk da haka yayin da ta fahimci damuwar al’ummar jihar Rivers, kungiyar ta bukaci su kwantar da hankalin su tare da ci gaba da bin doka da oda, tana mai jaddada cewa sauyi na hakika yana bukatar bin hanyoyin lumana da dimokuradiyya.
Kungiyar ta kuma bayyana goyon bayan ta ga Gwamna Siminalayi Fubara, tana mai karfafa masa gwiwa da ya tsaya tsayin daka wajen kare ka’idojin mulkin dimokuradiyya. Haka kuma ta yi kira ga hukumomin kasa da kasa musamman Majalisar Dinkin Duniya, da su sanya ido kan lamarin tare da daukar matakan da suka dace, don kare dimokuradiyya da hakkokin al’ummar jihar Rivers.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya