Kwamitin wuccen gadi na Majalisar Wakilai kan lura da harkokin jihar Rivers, ya gayyaci mai rikon mukamin gwamnatin jihar Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), da ya bayyana a gaban sa ranar Alhamis domin wata tattaunawa ta musamman.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar Akin Rotimi (Jnr) ya fitar a ranar Laraba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamitin mai mambobi 21, wanda Jagoran Majalisar Farfesa Julius Ihonvbere ke jagoranta, an kaddamar da shi ne a ranar Talata da ta gabata ta hannun Kakakin Majalisar Tajuddin Abbas.
An kafa kwamitin ne bayan da Majalisar Wakilai ta amince da kudurin Majalisar Dattawa na goyon bayan ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers, da shugaban kasa ya yi.
Rotimi ya bayyana a cikin sanarwar cewa kwamitin ya fitar da gayyatar ne a zaman kaddamar da shi da aka gudanar a ranar Laraba, 16 ga watan Afrilu 2025.
Ya ce zaman ya bai wa mambobin kwamitin damar tattaunawa kan rahotanni na farko da abubuwan da ke faruwa, tun lokacin da mai rikon mukamin gwamnan jahar ya hau kujerar mulki a jihar Rivers.