Labarai

Me Yasa Gwamnatin Enugu Ta Umarci Coci-coci Da Masallatai Su Cire Lasifika?

Gwamnatin jihar Enugu da ke Kudancin Najeriya ta umarci dukkanin majami’u da masallatai a jihar su cire duk wata lasifika da suka sa a wajen gine-ginensu cikin kwanaki 90, sannan kuma su dauki matakan tabbatar da cewa hayaniya ko karar abubuwan da ake yi a cikin wuraren ibadar ba ta fitowa waje.

An dauki matakin ne a yau Alhamis, a lokacin wani taro tsakanin hukumomin da shugabannin Kiristoci da Musulmi a jihar, kan aiwatar da tsarin gwamnatin jihar na takaita hayaniya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban hukumar raya babban birnin jihar ta Enugu, Uche Anya, wanda ya bayar da umarnin ya ce hayaniya da kara sun zama babbar matsala ga jihar.

Shugaban ya nuna takaicin yadda ofishinsa ya samu koke sama da 1,000, daga masu gidaje a kusa da wasu coci-coci da masallatai da wuraren rawa ko shaye-shaye da makamantansu a kan kara ko hayaniya da ke damunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button