December 9, 2024

`Kananan Hukumomi 14 Da Ke Cikin Hadarin Bala’in Ambaliyar Ruwa A Jihar Kano.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta yi gargadin cewa garuruwa 362 a kananan hukumomi 14 a jihar kano na cikin hadarin bala’in ambaliya.

Shugabar hukumar ta NEMA, Zubaida Umar, ce ta yi gargadin a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan zubar da shara da shirya tunkarar ambaliya, a Kano, ranar Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, hukumar kula da harkokin da suka shafi ruwa ta kasar ta yi hasashen cewa al’umma 3,749,200 na cikin hadarin ambaliya a jihar ta Kano.

Kananan hukumomin da ambaliyar za ta iya shafa a cewar hukumar sun hada da, Rimin Gado, da Tofa, da Kabo, da Madobi, da Garun Malam, da Bebeji, da Rano, da Dawakin Kudu, da Warawa, da Wudil, da da Sumaila, da Ajingi, da Kura da kuma Dala.

NEMA ta ce, bala’in ambaliyar da aka gani a 2012 da 2022, ya nuna muhimmancin hada hannu a tsakanin dukkanin matakan gwamnati wajen tunkara da magance bala’o’i.

Shugabar hukumar ta kuma jaddada muhimmancin wayar wa da jama’a kai kan hanyoyin zubar da shara da kuma ankarar da jama’a kan hadarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *