Labarai
Trending

Mutum 20 Sun Mutu 354 Sun Jikkata A Sudan Sakamakon Cutar Amai Da Gudawar Da Ta Barke.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Hukumomi a kasar Sudan sun sanar a ranar Lahadi cewa, barkewar cutar amai da gudawa ta yi sanadin mutuwar mutane kusan mutane sama da 20 tare da jikkata da dama.

Ministan lafiya Haitham Mohamed Ibrahim ne ya bayyana a cikin wata sanarwa in da ya ce, akalla mutane 22 ne suka mutu sakamakon cutar, kuma akalla mutum 354 ne aka tabbatar sun kamu da cutar kwalara a fadin lardin.

Sai dai ministan bai bayar da adadin lokacin mutuwar ko kididdigar ba tun farkon shekarar.

VOA ta ce, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an samu mutuwar mutane 78 ne daga cutar kwalara a bana a Sudan ya zuwa ranar 28 ga watan Yuli, cutar ta kuma raunata wasu fiye da 2,400 tsakanin 1 ga watan Janairu zuwa 28 ga watan Yuli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button