December 9, 2024

Sama Da Masu Zanga-zangar Tsadar Rayuwa 1,000 Ne Ke A Najeriya-Amnesty.

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Amnesty International, ta bayyana cewa sama da masu zanga-zangar tsadar rayuwa 1,000 ne ke tsare a hannun hukumomin Najeriya sakamakon shiga zanga-zangar tsadar rayuwa ta baya-bayan nan.

Zanga-zangar wadda aka gudanar tsakanin ranakun 1 zuwa 10 ga watan Agusta ta rikiɗe zuwa tarzoma a wasu sassan ƙasar, inda aka samu rahotannin sace-sace da lalata kadarorin gwamnati a wasu jihohi.

Hukumomin tsaro a Najeriyar sun ce sun kama mutane da dama da ake zargi da hannu a yamutsin.

To sai dai a cewar kungiyar ta Amnesty International, da dama daga cikin mutanen da aka kama waɗanda ba su aikata laifi ba ne.

Malam Isa Sanusi, daraktan ƙungiyar a Najeriya, ya ce an kama mutane mutum 632 a Jihar Kano, yayin da kuma a Sokoto an kama mutane za su kai 109 sannan kuma a Jihar Borno an kama mutum sama da 100.

“A Bauchi ma an kama mutane sannan kuma mun samu labarin cewa Kaduna ma an kama mutane za su kai 70, a Katsina ma mutum 70 aka kama.” in ji daraktan.

“To, mutanen dai suna rarrabe ne a duka jihohi, har yanzu ba mu gama ƙididdigewa ba amma zuwa yanzu ƙididdigar da muka samu kan mutanen da aka kama sun fi 100,” kamar yadda darektan ya bayyana.

Daraktan ya kuma ce “a duk lokacin da aka yi irin wannan zanga-zangar, muna sane da cewa ana yin kame na kan mai-uwa-da-wabi sannan ana kama mutanen da suka yi laifi da waɗanda ba su yi laifi ba inda a ƙarshe waɗanda suka shiga zanga-zangar ba tare da aikata laifin komai ba, sai a nemi wani laifi a laƙa masu wanda ba su aikata ba.”

An dai ga yadda zanga-zangar ta haifar da yamutsi a jihohin Kano da Jigawa da Kaduna da Katsina.

Wannan ya sanya aka ƙaƙaba dokar hana fita ta ba dare ba rana a jihohi da dama.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *