December 11, 2024

NAHCON ta ce kowanne alhajin 2023 za a mayar masa da naira 60,080.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa ta mayar da kuɗaɗen alhazan ne saboda rashin gamsuwa da wasu ayyukan da kamfanonin kasar Saudiyya suka gudanar.

Hukumar ta buƙaci alhazan da suka sauke farali a 2023 su tuntuɓi hukumomin alhazan jihohinsu ko kamfanonin jiragen yawon da suka bi, domin karɓar kuɗaɗensu.

Manema labarai a Najeriya sun rawaito cewa, sanarwar NAHCON ta ce kowanne alhajin 2023 zai sami naira dubu sittin da naira tamanin.

Shugaban Faransa ya yabawa Tinubu kan inganta ci gaban Najeriya.

Gwamnatin Najeriya za ta raba irin Alkama mai jure zafi ga manoma.

Sojan saman Nijeriya sun yi wa Ƴan Boko Haram fata-fata a Borno.

NAHCON ta ce ta miƙa naira biliyan 4.47 ga hukumomin kula da jin daɗin alhazan jihohi domin raba na alhazan da suka sauke farali a 2023.

Kamfanonin jiragen yawo 192 da aka tantance kuma an ba su jimillar Naira miliyan 917 domin mayar wa alhazansu.
Haka zalika shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullah Saleh Usman, ya kuma bukaci hukumomin yaƙi da almundahana (EFCC da ICPC) su sanya ido a kan aikin, domin tabbatar da gudanar da shi cikin tsafta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *