April 18, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

PSC, ta amince da ƙarin girma ga Kwamishinonin Ƴan Sandan Najeriya guda 20, da Mataimakan Kwamishinoni 19

Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC), ta amince da karin girma ga kwamishinonin ‘yan sanda guda 20, da mataimakan kwamishinoni 19, da sufetoci 13, da kuma mataimakan sufeto 14.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin a Abuja, ta hannun shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a Mista Ikechukwu Ani.

Ani ya bayyana cewa an daga darajojin kwamishinonin yan sandan zuwa Mataimakan Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (AIG), mataimakan kwamishina zuwa kwamishina, SP zuwa CSP, sannan DSP zuwa SP.

Daga cikin kwamishinonin da aka daga zuwa AIG akwai Fasuba Olabode, Musibau Ajani, Aliyu Musa, Patrick Atayero, Gyogon Grimah, Olaiya Mobolaji, da kuma Chukwudi Ariekpere.

Sauran sun hada da Abubakar Aliyu, Olalolu Adegbite, Godwin Eze, Disu Olatunji, Alausa Tolani, Kareem Musa, Mohammed Dalijan, da Dan-Mamman Shawulu.

Haka kuma akwai Clement Robert, Musa Mohammed, Thomas Nabhoni, Abel Miri Zwalchir, da Ifeanyi Uka.

Daga cikin mataimakan kwamishina da aka daga zuwa kwamishina sun hada da Usman Tahir, Sunday Okoebor, Ayodeji Faniyan, Saka Ajao, Omole Ola, Hope Okafor, da Ajo Ordue.

Sauran su ne Olufunke Adeayo, Stephen Ogedengbe, Iyabode Agbaminoja, Adebowale Lawal, Ojo Adekimi, da Yemi Oyeniyi.

Har ila yau akwai Obasi Okereke, Moses Ottah, Felix Nnebue, Gazali Abdul-Salaam, Fidelis Ogarabe, da Olubode Ojajuni.

Ani ya bayyana cewa duk jami’an da aka daga girman su ciki har da SP 13 da DSP 14, sun gabatar da kansu a gaban hukumar, inda aka gudanar da jarabawa da tattaunawa kafin a basu karin girma.

Shugaban hukumar malam Hashimu Argungu ne ya jagoranci shirin karin girman, tare da goyon bayan sauran mambobin hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *