Daga Isah Magaji Rijiya Biyu
Tun Bayan Wasanni 44 da ta yi ba tare da ta yi rashin nasara ba, ƙungiyar Bayer Leverkusen ta sake samun Nasarar fitowa zagaye na Gaba a Gasa mai Daraja ta Biyu ta Nahiyar Turai bayan ta doke West Ham.
A wani abu mai kama da a-rashi ƙungiyar kwallon ƙafa ta Atlanta tayi waje da Liverpool daga Gasar kofin Yurofa mai Daraja ta Biyu.
A dai gasar ta Yurofa kuma ƙungiyar AS Roma ta yi wajerod da kungiyar AC Milan.
Ita kuwa ƙungiyar Fiorantina ta kai wasan kusa da na karshe a gasar kofin Conference League.
Tun Bayan da Xavi ya bayyana cewar zai bar Horas da Barcelona a ƙarshen kakar wasan bana, ana ganin cewar ƙungiyar ta Barcelona ka iya maye gurbin sa da mai horarwa Rafa Marquez, cewar wakilin mu na bangaren wasanni.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ɗan Wasan Gaban Najeriya Da Napoli Osimhen Ya Nemi Chelsea Ta Rika Biyansa Fam £500, 000 Duk Mako.
-
Celta Vigo Na Jan Ragamar Laliga In Da Barcelona Ke Biye Mata A Mataki Na 2.
-
Liverpool Za Ta Yi Zawarcin Klyan Mbappe, Camavinga Ya Bar Tawagar Ƙasar Faransa.
-
Newcastle Na Son Ɗaukar Kelvin Philips Daga Manchester City.