Labarai
Trending

Rawar Karya Kwankwaso: Kotu Ta Yankewa Ƴan Daudu Hukunci Bayan Ta Same Su Da Laifin Yin Rawa Da Shigar Mata.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Kotun shari’ar addinin musulinci da ke zaman ta, a hukumar Hisbah ta jahar Kano a Arewacin Najeriya, ta yankewa wasu yan Daudu hukunci samun su yi shigar mata da kuma yin rawar karya kwankwaso a wajen bikin uban gidansu.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Mallam Sani Tamim Sani Hausawa, ta samu matasan ƴan Daudun da laifin bayan an karanto musu kunshin tuhumar da ake yi musu, inda nan ta ke suka amsa , sai dai sun roki kotun ta yi musu sassauci.

Mai shari’ar ya yanke musu hukuncin daurin watanni uku ko zabin biyan tarar naira dubu goma-goma kowannen su, tare da yi musu Bulala goma-goma, kamar yadda shafin Mujallar Hisbah na Facebook ya rawaito.

Gwamnatin Kano Za Ta Kwato Gine-gine Da Filayen Dutsen Dala Da Wasu Suka Mallakawa Kansu.

Gwamnatin Kano Za Ta Taimaki Manoma Da Masu Kiwo Cikin Kasafin 2024,- KNARDA.

Ɗaruruwan Ƴan Ƙaramar Hukumar Dala Za Su Amfana Da Ilmin Kwamfuta A Kyauta.

Tunda farko dai hukumar Hisbah ce ta kama matasa ta kuma gudanar da su, Mukaddashin kwamandan hukumar Hisbah na jahar Dr. Mujahiddin Aminuddin Abubakar , ya bayyana cewa hukumar ba zata gajiya ba , wajen dakile aiyukan Baɗala , domin aikin hukumar shi ne ,yin hani da aikata mummuna tare da kiran aikata kyakkyawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button