Daga Isa Magaji Rijiya Biyu
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Newcastle United ta bayyana cewa tana da Sha’awar ɗaukar ɗan wasan Manchester City Kelvin Philips a Junairu mai zuwa.
Ita kuwa Manchester United ta tabbata da cewa za su raba gari da Jordan Sansho a watan na Junairu 2024.
Ƙungiyar Getafe FC ta ce tana son ɗaukar Marson Greenwood amatsayin na dindin.
Ya yin da ƙungiyar Al_ittihad ta ƙasar Saudiyya za ta naɗa sabon me horaswa Marcelo Gallerdo.