April 18, 2025

Ana zargin makiyaya sun hallaka manoma biyu a jihar Benue.

Wasu mutane dauke da makamai da ake zargin makiyaya ne sun kashe manoma biyu, a hare-hare daban-daban da suka faru a wasu ƙauyukka da ke ƙaramar hukumar Gwer ta yamma a jihar Benue.

Wakilin mu ya tattara rahoto daga wata majiya a yankin, wadda ta nemi a ɓoye sunan ta cewa, makiyaya ne suka kashe waɗanda lamarin ya shafa a kan hanyar da ke kaiwa hedikwatar ƙaramar hukumar.

A cewar majoyar, “Ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe an hallaka shi ne a ranar Laraba a ƙauyen Atukpu, kimanin kilomita ɗaya daga hedikwatar ƙaramar hukumar, yayin da aka kashe ɗaya a kan hanyar Naka-Adoka a wannan rana.

“Yanzu haka da nake magana da kai, makiyayan sun mamaye hanyar Makurdi-Naka, wadda yanzu babu kowa a kanta saboda tsoron harin, ” yana mai ƙarawa da cewa masu babura da ake kira ‘Okada’ ne suka gano gawarwakin waɗanda aka kashe.

Da aka tuntube shi shugaban ƙaramar hukumar Gwer ta yamma Victor Ormin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa ɗaya daga cikin mutanen da aka kashe yana kan hanyar Taraku-Naka inda yake kokarin samo kayan rufin gidan sa.

Ya ce ɗaya kuma an kashe shi ne a yankin Adoka Naka, yana mai jaddada cewa kashe-kashen sun fara zama ruwan dare a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *